Sallar idi ita ce taron da ake yi sau biyu ko sau uku a
shekara, watau a ƙaramar Sallah, saboda murnar ƙarewar azumin watan
Ramalan lafiya, da kuma Babbbar Sallah, saboda murnar ƙarewar aikin
hajji lafiya. A wasu wuraren kuma ana yin Sallar Gani, ko Sallar
Mauludi, don tunawa da ranar da aka haifi Manzon Allah, Annabi Muhammadu
( tsira da Amincin Allah Su tabbata a gare shi). Sai dai ita wannan
sallar ba a yi mata idi, watau ba a zuwa bayan gari a yi raka’o’in
sallah.
Tun kafin jajibirin sallolin nan ake ta yin kintse-kintse, ana
tattalin harkokin sallah, ana dake-dake, da sayen bisashe, da sauran
kayan jin daɗi. A daren jajibiri ake ta yi wa sarakunan gargajiya
bushe-bushe da kaɗe-kaɗe, ko buga tambari, ko a daka (bindiga) saboda a
sanar da cewa go be sallah. Kowane babban mutum yakan sanar ta hanyar
gangami, ko aikawa da kar-ta-kwana, da sauran hanyoyin sadarwa irin na
gargajiya.
A safiyar sallah akan yi ta raba tuwaye kuma ‘yan’ uwa da maƙwabta
sukan tara abinci iri-iri a gidan ɗayansu, a taru a ci tare wuri ɗaya,
ana ci ana raha. Idan ƙaramar Sallah ce, akan ci abincin tun kafin a
tafi Masallacin Idi. Amma idan Babbar Salla ce, sai an sauko Idi. Wajen
abinci kuwa, kowane mai gida yakan yi iyakar ƙoƙarinsa gwargwadon
ikonsa, ya ga dai ya fifita abincin sallah, ya daɗaɗa shi fiye da wanda
ya saba ci yau da kullum.
Ahantsin ranar idi, mutane sukan fita; har da yara da tsofaffi, su
tasar wa filin idi a bayan gari, inda za a jira sarki, da limamin gari
don sallah. Ana cikin jira ne sarki da baradensa, da hakimansa, na kusa
da na nesa sukan iso a kan dawakai da taguwoyi, kowannensu ya ci ado,
suna tafiya suna takama saboda murnar zuwa Masallacin Idi da kewayowar
wannan rana.
Da zarar sarki ya isa masallaci sai a tsayar da sallah, a yi raka’o’i
biyu a sallame. Wasu mutane su yi tafiyarsu, wasu kuma su dakata don su
saurari huɗubar liman, wadda galibi yake gargadin jama’a, da jawo
hankalinsu zuwa ga kulawa da addini, da tuba ga Allah, tuba ta sosai, da
gyara halaye, da lura da wa’aztuwa da juye-juyen zamani da sauran
irinsu.
Bayan ya ƙare huɗuba, sai kowa da kowa ya kama gabansa, ya tafi gida
ya ci gaba da hidimar sallah. Sarki da manyan mutane sukan bi wata hanya
ba wadda suka biyo da farko ba, saboda kowa da kowa ya sami damar ganin
su, don su yi murna da ganin sarki da kewayowar wannan rana mai
albarka. A daidai wannan lokaci kuma, wasu jama’a maza da mata, yara da
manya, suna can suna taruwa kan wuri a fadar sarki, suna jiran sa. Idan
sarki ya isa fada tare da jama’arsa, sai ya hau sama idan a birni ne,
don mutane su gan shi, shi kuma ya gan su ya yi musu jawabin cikar
shekara, inda yake jan kunnuwansu da hada kai da son zumunta da zama
lafiya, da kula da aiki da addini, da al’ada, da ladabi da biyayya ga
magabata, da cika alƙawari, da tsare mutunci, da kula da tsabtar jiki
data gidaje da sauransu, Bayan sarki ya yi jawabi, sai ya shiga gida ya
zauna a kan karagar mulki, hakimai da duk mutane suna tafiya dai-dai
suna gaisuwa yana karɓa. Idan ƙauye ne sai kawai ya shiga soro ba da ya
hau ko’ina ba, ana zuwa wurinsa yana karɓar gaisuwa.
Wannan taro, na farkon rana, ya fi cika a ƙaramar Sallah,saboda rashin hidimar yanke-yanken dabbobin layya.
Da an ce marece ya yi, sai dandalin gidan sarki ya cika da mutane
faƙil, ko’ina, ba masaka tsintsiya, ana ta kade-kade da bushe-bushe.
Samari da ‘yammata ana kalankuwa, ana darawa, ana tafawa ana murna, da
farin ciki. Yara kuma su yi ta zaci sunakai da komowa harwajen
kwanabiyar ko bakwai.
Yawon Sallah: Mutane suna zuwa suna gai da ‘yan’uwa da abokai da
surukai, don taya su murnar kewayowar ranar sallah. Su kuma sukan ba su
goron sallah. Yara da yawa sukan mayar da yawonsalla tamkar wani abin ku
zo ku gani suna shiga gida-gida, suna kaɓiar abin yawon sallah, kuma
suna tafiya suna yi wa juna ba’ar raha iri -iri.
Rana ta biyu, a kashegarin sallah, sai sarki yakan yi hawa, wanda ake
kira hawan sarki, ya kuma ci gaba da hawan har kwana uku don ya sadu da
mutanensa, ya ga wasu wurare. Wannnan hawa, a wasu wurare sunansa hawan
daushe , ko hawan bariki.
Shi ke nan, sai a ci gaba da shagulgulan sallah har ‘yan kwanaki, sa’annan kowa ya koma ga harkar gabansa ta yau da kullum.
“Sallah bukin ɗaya rana! Sallah mai yawan baya, kin wuce kin bar wawa da bashi!”