python books bayani acikin harshen turanci pdf

python leaning book1
python leaning book 2
python leaning books 3

Python pdf acikin harshen turanci

python pdf

NASIHOHI GA AL'UMMAR MUSULMI

NASIHOHI GA AL'UMMAR MUSULMI

Ya inganta cikin ruwayoyin musulinci cewa: Duk wani aki baya inganta sai da niyya. sa'an nan kuma yin aikin alhairi domin Allah shine mafi alhairi ga musulmin kwarai, domon duk wani aiki da aka yi ba don Allah ba to zai zama cikin dayan biyun nan ne ko dai yi ne don a gani wato riya,ko yi don Allah kuma duk wanda yayi wani aiki don a gani a yaba masa ba don Allah ba to yayi banza.{gwamma ma da bai yi ba} saboda haka du abinda zamu yi to murika kayautata niyya.

A mu'amalar mu musamman da iyalai da kuma abokan huldarmu ta yau da kullum to mu rika sanya hakuri da bayyana kyawawan dabi'u, don an ce: mafiya yawan Mutanen da suka musulunta wajen Manzon Allah kyawawan dabi'u suka gani daga wajensa har suka yi sha'awar shigowa cikin musuluncin.saboda haka ba komai ne idan anyi maka ko an yi maki shikenan sai a dauki fushi ba.

fushi yana daga cikin halayyan zuciya masu fandarewa daga tafarci madai-daici. wani marubuci yana cewa:"Idan fushi ya yi galaba akan mutum har ya dabai-baye shi to sai ya fara tunkaho, yana sabo yana kuma keta haddi". ya kuma kara da cewa shi fushi wani shamaki ne da yake kange hhankalin mutum ya kuma zare masa karfin fahimtar hakikka, mai fushi yakan kidime har ya iya bayyana halayya irin na Dabbobi.

Abu ne sanan ne cewa: sakamakon da fushi yake haifarwa shine nadama.Imamin mu na Ahlul-baiti {A.S} Imam Ja'afar Assadiq {A.S} yana cewa: " fushi yana zagwanyar da zuciyar mai hikima, Duk wanda bai mallaki fushinsa ba, to bai mallaki hankalinsa ba".

Imam Ali {AS} yana cewa: "ka kiyayi fushi farkonsa hauka ne, kakshensa kuma nadama ce". musammman a rayuwar aure ta zaman yau da kullum dole a samu sabani da kuskure tsanin ma'aurata, saurin fushi da daukan mataki yakan kai ga haifar da babbar matsalar da ta hada da kace-na-ce, duka lalata dukiya kai har da ma saki. hadiye fushi kuwa siffa ce da take nuna jarunta da kuma suffantar da siffa irin ta bayin Allah na gari. saboda haka aikata ta zai bada matukar gudummawa wajen samar da zaman lafiya tsakanin ma'aurata.domon dole yau da kullul a samu sabani ttasakanin ma'aurata in kuwa ba'a yi hakuri da hadiye fushi ba, to kullum fa ba za su kare ba.

Manzon Allah {S.A.W.} yayi wasiyya da gargadi game da fushi idan yayi galaba akan mutum to ya gabatar da wadan nan abubuwan........"idan har irin wan nan ta samu dayanku idan yana tsayene ya zauna, idan kuwa yana zaune ne to ya kwanta, idan bai gushe ba to yayi alwala da ruwa mai sanyi ko kuma yayi wanka domin ba abin da ke kashe wuta sai ruwa.

Afuwa na daga cikin kyautatawa. a wurare da dama cikin Al'kur'ani mai tsarki Allah yana yabo da son masu kautatawa. saboda haka a duk lokkacin da aka sami sabani yaya da kyau ayi afuwa. Imam Ja'afar Assadiq yana cewa: "yin afuea alhali akwai ikon ramuwa yana daga cikin sunnar Mnzanni {A.S}.

Imam Ali {A.S} yana cewa: " ka fadakar da dan uwanka aibinsa ta hanyar kyautata masa, kuma ka maida sharrinsa ta hanyar yin alhairi gareshi". wani marubuci yana cewa: "Afuwa da kaskantar da kai suna tasiri kyarai wajen shawo kan Abokin gaba har ma ta sa shi ya sauya tunanin sa, da halayyansa". wannan abokin gaba kenan to yaya muke zato ga abokin zama? saboda haka afuwa wani babban makami ne na inganta zaman ma'aurata, da kuma mu'amular mu da jama'a ta yau da kullum.

Kazalika ba a kan komai ake yin magana ba. domin yawaita magana akan komai to yana saurin kawo raini musamman da wanda ake magana da shi din, ko da ita din. kuma ba akan komai ake yin shuru ba don yin shuru akan komai yana kawo matsaloli masu wanzuwa. wadansu matsalolin magana akan su shi ke magance su, wasu kuma shiru shi ke kawar da su,wasu matsalolin tafiya taer da su shine mafi sauki domin dolie ne tafiya da matsala.sai dai yadoru akan ka ko akan ki don gano matsalar ku da yadda zaku bullo mata don magance ta.

Uzuri..........wato {Daga kafa} ko lamuni a inda ya dace yana sa aga Mutun da Daraja, rashin sa kuwa yana zubar da gima.

hakuri akan abinda ya dace kuwa yana kawo nasara da daukaka a duk bangarorin rayuwa,rashin sa kuwa yana kawo gazawa da Nadama.

Zamantakewa na matukar bukatar kawaici a lokacin da ya kamata, rashin sa kuwa yana haddasa husuma.

Idan za ka so Mutum to kada ka tsananta Soyayyar domin wata rana yana iya zama makiyinka. haka idan za ka ki Mutum kada ka tsananta kiyayyar don watan wata rana yana iya zama masoyinka ko masoyin ki.

Nau'in Macen da ya kama mai saiti ya aura: musamman a halin da ake ciki yanzu a akasar nan Nijeriya, idan mutum ya je ya kwaso mai kwadayin abin Duniya shi zai yaba wa aya zakinta wato 'yar jari-hujja wanda ake ce masu {Capitalism} ko {Materialistic} don haka yana da kyau musamman matasi {Saurayi} kai da baka riga ka yi aure ba, kaso wacce zaku hadu ku rufa wa juna asiri, ba wacce za ta yi ta soya maka aya a tafin Hannu ba ta hanyar dora maka wadansu larurori da suka fi karfin ka kuma ka wahala sannan babu lada ba la'ada.bance kada ayi wa iyali hidima ba, A'a abinda nake cewa shine:{ayi dai-dai gargwadon halin da ake da shi a wannan lokacin} babu cuta babu cutarwa. lallai nasan kowa yana son shgali to amma akan lura da yanayi ko halin da maigida yake ciki ne ko yake da shi ne da kuma kasar gaba daya. ku kuma maza don Allah a rinka kwatanta adalci, iadan an samu canji Iyalai ma ya kamata su shaida kada kada ka manta amance aka baka.don shi aure son juna
ne, tasayinjuna ne, da rufa wa juna asiri bai kamata a cutar da juna ba.

Rashin wadatar zuci wani marubuci yana cewa: tun ran da mutum ya zo Duniya, to bukatu iri-iri da ban da ban suka yi masa kawanya. wasu daga ciki sune muhalli da tufafi duk laruurori ne ga ci gaban Dan Adam wasu bakatun kuma ba larurori ba ne da'iman suna sauyawa kuma ba'a taba biyan su duka saboda haka matukar rashin wadatar zuci ya kutso cikin gidan ka musamma ta dira a kan matar gida to kullum bazata wadatu da abinda mai gida ke kawo mata ba, musamman a cikin irin halin da azzaluman shugabanni suka saka jefa kasar nan a ciki. to idan hakan ta faru babu abinda zai biyo baya sai rainuwa, shi kuma Namiji yana ganin cewa ai yana iya bakin kokarinsa ita kuma tana raina masasaboda haka sai sabaani da matsaloli su yi ta faruwa.kwadayi yana daya daga cikin abubuwan da ke haifar da wadatar zuci Imam Ali {A.S} yana cewa: " ku kiyayi kwadayi domin ma'abocinsa jingina nne ga kaskanci da wahala". kwadayi yana kashe zuciya kuma yana bata addini kuma yana
Bal-baltar da kuricciya". saboda haka kwadayi ciwo ne na ruhi mai hatsari da bashi da magani sai karkashin Imani da Allah da kuma ranar llahira saboda haka ma'aurata sai ayi hattara lallai kwadayi in ya shiga giga yakan tarwatsa zaman lafiya kuma ya shuka matsaloli da rashin fuskantar hakikanin abinda ya dace don don kuwa kwadayi wata irin sha'awace da kan kai mutum ga kaskanci da wulakanci. wadatar zuci ta hanyar da za'a iya magan ce wan nan matsala . A duk lokacin da mutum ya ji cewa Alhamdulillahi ya gamsu da duk halin da ya samu kansa a ciki ba tare da hankoron sai ya cimma na sama da shi ko ta halin kaka ba, to lallai wannan zai samu kwanciyar hankali da zaman lafiya.Imam Ali {A.S} yana cewa: "Mafi hankali shine wanda ya riki rashin jiran tssammani ya lizimci wadatar zuci da takawa ya kuma rabu da mai kwadayi".
Wadatar zuci task ace wadda bata karewa, ma’abocinta yana neman gwargwadon biyan bukatar rayuwarsa ne kawai, kuma yana tsara al’amuransa na rayuwa ya dai-daita suta hanyar aiki da hankalinsa. Baya dulmiyar da zuciyarsa wurin neman kari ko ta halin kaka yakkan wadatu da abin da yasamu ta hanyar halal kawai. Saboda haka ma’aurata musamman mata ku samu wadatar zuci da godiya akan duk abinda mai gida ya kawo muku. Wannan zai say a ji dadi ya kuma yi burin kara muku, hakan kuma zai kara maku dankon zumunci da soyayya da zaman lafiya a tsakaninku.

Sai kuma abu na kusan karshen Magana ta wanda kusa ya fi duk abubuwan da na yi Magana akansu wato Mummunan zato: sau da yawa rashin kyautata zato yakan zama babban makami na haifar da fititunu atsakanin al’umma. Mummunan zato na daga cikn cutuutukan ruhi masu hadari. Shine tushen kowane asara, bata da kuma fandarewa, sharri ne mai ciwo da kuma azabtar da ruhin mutum. A kullum mai mummunan zato za ka same shi a cikin radadi na zuciya da rashin kwanciyar hankali.ya zo acini Al’kur’ani mai tsarki cewa: ‘Ya ku wadanda kuka yi Imani ku nisanci yawan zato domin wani zato zunubi ne’ ya kuma zo a cikin hadisin Manzon Allah cewa: Jinin Musulmi ga musulmi haramun ne da dukiyarsa da kuma yin maummuna zato a gareshi’ har ila yau Imam Ali {A.S} A cikin Nahjul-Balagah yana cewa: game da mummuna zato “Yankewa wanda aka amince da shi hukunci akan zato ba adalci ba ne” saboda haka yin mummunan zato ga mautane na kwarai aiki ne na zalunci, saboda haka
yana da kyau ma’aurata su guji yi wa juna mummunan zato domin da yawan matsalolin aure mummunan zato ke taimakawa wajen haifar da su. Saboda haka yi wa junakyakkyawan zato yana habaka da kulla kauana tsakanin ma’aurata da hadin kai. Imam Ali {AS} yana cewa: “ Duk wanda ya yi kyakkyawan zato ga mutane to za su so shi” har way au dai Imam Ali {AS} yana cewa: shi kyakkyawan zato hutun zuciya ne da kubutar da addini” Imam Ja’afar Assadiq {AS} yana cewa kyautata zato hakkin musulmi ne akan musulmi in day ace: yana daga hakkin mumin akan mumini ….kyautata wa juna zato….kuma kada ya karyata shi” saboda haka ma’aurata a sani ceawa kyakkyawan zato wani hhakki ne akan juna , samara da shi wajibi ne kuma ci gaba da wanzar da shi ci gaban zaman lafiya ne da kwanciyar hanhali ga ma’aurata. Saboda haka dan Allah Duk ayi kokarin ganin an kiyaye.

YANDA AKE DAUKAR SNAP CAPTURE A KWAMFUTA (PC)

sing the default keyboard shortcuts

Quick tips:
  • Your keyboard’s Print Screen key copies your current screen. You can then paste it into image editing software with Ctrl + V.
  • Pressing Alt + Print Screen will capture only the currently selected window.
Taking a screenshot is simple, regardless of which version of Windows you’re running. There are only a few steps — assuming you haven’t fiddled with the default keyboard controls — and if you need some free image editing software to tweak them, these are our favorites.
Step 1: Capture the image — Assuming the area you want to capture is displayed on your screen, press the “Print Screen” (often shortened to “PrtScn”) key, typically located in the upper-right corner of your keyboard, to capture a screenshot of your entire display. Alternatively, press “Alt + Print Screen” to capture a screenshot of the active window. If you’re on a laptop, you may need to press “Fn” + “Print Screen” if your laptop has another feature assigned to that particular key.


There will be no noise or any other indication the screenshot was taken, but the resulting image will be saved as a PNG file to your clipboard. If using Windows 8 or 10, press the Windows Key + Print Screen to automatically save a full-screen screenshot within the “Screenshots” folder of your picture directory.
Alternatively, if you have Dropbox installed, the screenshot will be automatically deposited in your Dropbox directory, under Screenshots.
Step 2: Open Paint — In Windows 10, you can open the Start menu, go to “All Apps”, and scroll through the alphabetical list until you find Paint.


In Windows 8, press the Windows key to open the start screen. Afterward, click the down arrow in the bottom left, press “Ctrl” + “Tab,” or swipe downward from the center of the display to access the Apps View. From there, select Paint.
For Windows 7, click the Start menu, navigate to the “Accessories” folder  and click “Paint”. The icon depicts a painting palette with a brush on the right side, but it will vary slightly depending on your operating system.
All three iterations of Windows also include Windows Search, which can be used to find Paint by searching for — you guessed it — “Paint.”
Step 3: Paste the screenshot — Once open, click the “Paste” button in the upper-left corner of the program, choose “Edit” then “Paste”, or press “Ctrl + V” on the keyboard to paste your screenshot. Again, the exact navigation and wordage will vary slightly in different versions of Windows, but the keyboard shortcut will remain the same.





SALLOLI BIYAR NA YINI SUNA KARA LAFIYA MAI INGANCI GA JIKIN DAN ADAM.

SALLOLI BIYAR NA YINI SUNA KARA LAFIYA MAI INGANCI GA JIKIN DAN ADAM.  Hakika Salloli biyar da mukeyi ayini a kowace suna  karawa dan Ada...