AURE








AURE

Aure alaƙa ce ta haliccin zaman tare tsakanin namiji da mace. Ana yin sa ne saboda abin da aka haifa ya sami asali, da mutunci, da kiwon iyaye. Kuma shine maganin zina da ‘ya’ya marasa iyaye. Aure muhimmin abu ne ga al’umma. Saboda haka akwai hanyoyi ayyanannu na tabbatar da shi.
Idan yaro ko yarinya suka girma sai iyayensu su sa ransu su yi musu aure tun ransu bai yi halinsa ba.
Wani lokaci kuwa yaro ne yake ganin yarinya ya riƙa yi mata ‘yar kyauta har a gane yana son ta, sai a nemar masa ita, ko abokansa su faɗa wa iyayensa a gida cewa sun ga alamar Wane yana son Wance. Ko kuma a faɗa wa yarsa ko gwaggonsa, ko matan wansa, su kuma su isar da saƙon ga iyayensa.


   Aure,
    abune wanda ake yi tsakanin mace da namiji domin gudanarda wata sabuwar rayuwa tsakanin na miji da amce.
  Aure,
  abune wanda ake yinsa badan rabuwa da juna ba ko zama na dan wani lokaci shi aure anayinsane da niyar zama har abada tareda juna. 

No comments:

Post a Comment

SALLOLI BIYAR NA YINI SUNA KARA LAFIYA MAI INGANCI GA JIKIN DAN ADAM.

SALLOLI BIYAR NA YINI SUNA KARA LAFIYA MAI INGANCI GA JIKIN DAN ADAM.  Hakika Salloli biyar da mukeyi ayini a kowace suna  karawa dan Ada...