AL'ADU

AL’ADUN HAUSAWA

Hausawa mutane ne masu tsananin rikon al’adunsu na gargaiiva, musamman wajen tufafi, da abinci, da al’amuran da suka shafi aure ko haifuwa, ko mutuwa, da sha’anin mu’amala tsakanin dangi da abokai da sbuwagabaam da sauransu, da kuma al’amuran sana’a ko kasuwanci ko neman ilimi.
Tun daga zuwan Turawa har yau, Hausawa suna cikin al’ummomin da ba su saki tufafinsu na gargajiya su ari na baki ba. Galibin adon namiji a Hausa ba ya wuce riga gari, da wando musamman tsala, da takalmi faɗe ko ƙafa-ciki, da hula ƙube, ko dankwara, ko dara. In kuma saraki ne ko malami ko dattijo, yakan sa rawani. Adon mata kuwa, zane ne, da gyauton yafawa, watau gyale, da kallabi, da taguwa, da ‘yan kunne, da dutsen wuya, watau tsakiya. A da can, suna sa ɗan hanci, amma yanzu wannan adon ya ƙaura.
Yawancin abincin Bahaushe kuwa, ana yin sa da gero ko dawa ne. Sai kuma sauran abubuwan haɗawa, da na marmari, kamar su wake da shinkafa da alkama, da kayan rafi, da sauransu.
Yawancin Hausawa Musulmi ne, saboda haka yawancin al’adunsu da suka shafi aure da haifuwa da mutuwa, duka sun ta’allaƙa da wannan addini. Sai ɗan abin da ba a rasawa na daga al’adun gargajiya, musamman a wajen Maguzawa.
Haka kuma wajen mu’amala da iyaye ko dangi ko abokai, ko shuwagabanni ko maƙwabta ko wanin waɗannan yawanci na Musulunci ne. Kazalika sha’anunuwan sana’a da kasuwanci da neman ilimi, duk ajikin Musulunci suka rataya,
Can ainihi, sana’a da kasuwanci da neman ilmi suna bin gado ne. Watau kowa yana bin wadda ya gada kaka da kakanni. Kuma idan mai sana’a ya shiga baƙon gari, zai je ya sauka a gidan abokan sana’arsa ne. In ma koyo ya zo yi, zai je gidan masu sana’ar gidansu ne. Saboda haka kusan kowace sana’a akwai sarkinta, da makaɗanta, da mawaƙanta, kai har ma da wasu al’adu na masu yinta da suka sha bamban da na sauran jama’a.
Bauta da barance a wurin Bahaushe ba munanan abubuwa bane, musamman dangane da sha’anin koyon sana’a. Bawa yana fansar kansa ta hanyar sana’a. Kuma mai koyon sana’a yana yin barance a gidan mai koya masa ne. Irin wannan almajircin, ana kiran sa bauta. Duk mai wata sana’a, ko ɗan kasuwa, ko malami, yana alfaharin a ce ga wasu sun koya a wurinsa har sun ƙasaita, ko ma har sun fi shi. Su kuma duk irin maƙamin da suka samu, ba za su raina shi ba. Za su riƙa yi masa ladabi.

No comments:

Post a Comment

SALLOLI BIYAR NA YINI SUNA KARA LAFIYA MAI INGANCI GA JIKIN DAN ADAM.

SALLOLI BIYAR NA YINI SUNA KARA LAFIYA MAI INGANCI GA JIKIN DAN ADAM.  Hakika Salloli biyar da mukeyi ayini a kowace suna  karawa dan Ada...