KASHE-KASHEN AURE
Aure ya kasu kashi-kashi. Akwai auren soyayya; da auren tilas, da
auren zumunta, da auren sadaka, da auren ɗiban wuta, da auren
dangana-sanda, da, auren gayya, da auren ɗiban haushi ko ɗiban takaici,
da ɗiban tsiwa ko kece raini, da kashin ƙwarnafi, da sauran irinsu.
Auren Soyayya: Aure ne wanda yaro ke ganin yarinya
ya ce yana sonta da aure, ita kuma ta amince, iyayenta ma su yarda da
maganar, kana a yi haramar ɗaurin aure.
Auren Tilas: A nan, yaro yakan ga yarinya ne, ya ce
yana son ta da aure, amma ba ta amince ba. Iyayenta kuma su zartar da
hukunci, walau wasu na so, ko suna ƙi. Har ma akan ba da yarinya ga
wanda yake sa’an mahaifinta ne, ko sa’an kakanta, alhali kuma ba ta so.
Kuma akan nema wa yaro yarinya ba tare da yana so ba, saboda wata alaƙa
ko yarjejeniya tsakanin iyayensu. Wannan ma auren tilas ne.
Auren Zumunta: Wannan aure ne wanda akan nema wa
yaro yarinya daga cikin dangin uwa ko na uba, ba tare da an shawarci
yarorn ko yarinyar ba. Irin wannan aure, ana yin sa ne don ƙara yauƙaƙa
danƙon zumunta tsakanin ‘yan’uwa.
Auren Sadaka: Shi kuma aure ne da ake bayar da
yarinya ga wani, saboda neman tubarraki, kamar irin sadakar da ake ba
malamai, almajiransu, musamman idan yarinya ta girma bata sami manemi da
wuri ba. Ana kuma yin auren sadaka don gudun kada ta jawo wa iyayenta
abin kunya. Wani lokaci kuma idan mutum bai sami haihuwa da wuri ba,
yakan yi alƙawarin cewa, zai ba da ita sadaka in ya samu. Yakan ba wani,
ya ce, in ya sami ‘ya har ta rayu, zai yi sadaka da ita.
Auren Ɗiban Wuta: Bayan an saki mace saki uku,
alhali kuwa matar tana son mijinta, shi ma yana son ta, dole sai ta auri
wani mutum, kafin ta sami damar komawa ga mijinta na farko. To, auren
nan da ta yi, da ƙudurin cewa za ta dawo wurin mijinta na da, wannan shi
ne auren ɗiban wuta.
Auren Dangana-Sanda: Mutum yakan auri matar da ke
zaune a gidan kanta; Sai ya zamana ba za ta iya tasowa ta zo gidansa ta
zauna ba, saboda waɗansu dalilai. Haka shi ma ba zai iya zuwa gidanta ya
zauna ba. Sai dai ya riƙa zuwa can gidanta yana kwana. Irin wannan
aure, abinda ya sa ake kiran sa auren dangana-sanda, wai saboda maigida
yana dangana sandarsa a bakin kofar dakinta ne, kana ya shiga ya kwana.
Auren Gayya: Idan matar mutum ta fita, alhali kuwa
yana son ta, ya dai sake ta ne don ta addabe shi, to maza sai ya yi
sauri ya yi wani aure kafin ya sake ta, ko kafin ta gama idda. Ba don
komai zai yi wannan auren ba, sai don kurum ya fashe haushinsa, ko kuma
don kada matar ta riga shi yin aure.
Auren Ɗiban Haushi: Ana kuma kiran sa auren ɗiban
takaici, ko auren ɗiban tsiwa, ko na kece raini da kashin ƙwarnafi. Idan
matar mutum ta dame shi da fitina, yakan tashi takanas ya je ya auri
wata mace mai kyau ko dukiya ko asali ko addini, fiye da wadda ke
gidansa, ko wadda ya saki. Ana yin wannan aure don kawai fashe haushi ko
ɗebe takaici ko don a gusar da walakanci da raini da tsiwace tsiwace
na ba gaira ba dalili.