SALLAR IDI

SALLAR IDI

Sallar idi ita ce taron da ake yi sau biyu ko sau uku a shekara, watau a ƙaramar Sallah, saboda murnar ƙarewar azumin watan Ramalan lafiya, da kuma Babbbar Sallah, saboda murnar ƙarewar aikin hajji lafiya. A wasu wuraren kuma ana yin Sallar Gani, ko Sallar Mauludi, don tunawa da ranar da aka haifi Manzon Allah, Annabi Muhammadu ( tsira da Amincin Allah Su tabbata a gare shi). Sai dai ita wannan sallar ba a yi mata idi, watau ba a zuwa bayan gari a yi raka’o’in sallah.
Tun kafin jajibirin sallolin nan ake ta yin kintse-kintse, ana tattalin harkokin sallah, ana dake-dake, da sayen bisashe, da sauran kayan jin daɗi. A daren jajibiri ake ta yi wa sarakunan gargajiya bushe-bushe da kaɗe-kaɗe, ko buga tambari, ko a daka (bindiga) saboda a sanar da cewa go be sallah. Kowane babban mutum yakan sanar ta hanyar gangami, ko aikawa da kar-ta-kwana, da sauran hanyoyin sadarwa irin na gargajiya.
A safiyar sallah akan yi ta raba tuwaye kuma ‘yan’ uwa da maƙwabta sukan tara abinci iri-iri a gidan ɗayansu, a taru a ci tare wuri ɗaya, ana ci ana raha. Idan ƙaramar Sallah ce, akan ci abincin tun kafin a tafi Masallacin Idi. Amma idan Babbar Salla ce, sai an sauko Idi. Wajen abinci kuwa, kowane mai gida yakan yi iyakar ƙoƙarinsa gwargwadon ikonsa, ya ga dai ya fifita abincin sallah, ya daɗaɗa shi fiye da wanda ya saba ci yau da kullum.
Ahantsin ranar idi, mutane sukan fita; har da yara da tsofaffi, su tasar wa filin idi a bayan gari, inda za a jira sarki, da limamin gari don sallah. Ana cikin jira ne sarki da baradensa, da hakimansa, na kusa da na nesa sukan iso a kan dawakai da taguwoyi, kowannensu ya ci ado, suna tafiya suna takama saboda murnar zuwa Masallacin Idi da kewayowar wannan rana.
Da zarar sarki ya isa masallaci sai a tsayar da sallah, a yi raka’o’i biyu a sallame. Wasu mutane su yi tafiyarsu, wasu kuma su dakata don su saurari huɗubar liman, wadda galibi yake gargadin jama’a, da jawo hankalinsu zuwa ga kulawa da addini, da tuba ga Allah, tuba ta sosai, da gyara halaye, da lura da wa’aztuwa da juye-juyen zamani da sauran irinsu.
Bayan ya ƙare huɗuba, sai kowa da kowa ya kama gabansa, ya tafi gida ya ci gaba da hidimar sallah. Sarki da manyan mutane sukan bi wata hanya ba wadda suka biyo da farko ba, saboda kowa da kowa ya sami damar ganin su, don su yi murna da ganin sarki da kewayowar wannan rana mai albarka. A daidai wannan lokaci kuma, wasu jama’a maza da mata, yara da manya, suna can suna taruwa kan wuri a fadar sarki, suna jiran sa. Idan sarki ya isa fada tare da jama’arsa, sai ya hau sama idan a birni ne, don mutane su gan shi, shi kuma ya gan su ya yi musu jawabin cikar shekara, inda yake jan kunnuwansu da hada kai da son zumunta da zama lafiya, da kula da aiki da addini, da al’ada, da ladabi da biyayya ga magabata, da cika alƙawari, da tsare mutunci, da kula da tsabtar jiki data gidaje da sauransu, Bayan sarki ya yi jawabi, sai ya shiga gida ya zauna a kan karagar mulki, hakimai da duk mutane suna tafiya dai-dai suna gaisuwa yana karɓa. Idan ƙauye ne sai kawai ya shiga soro ba da ya hau ko’ina ba, ana zuwa wurinsa yana karɓar gaisuwa.
Wannan taro, na farkon rana, ya fi cika a ƙaramar Sallah,saboda rashin hidimar yanke-yanken dabbobin layya.
Da an ce marece ya yi, sai dandalin gidan sarki ya cika da mutane faƙil, ko’ina, ba masaka tsintsiya, ana ta kade-kade da bushe-bushe. Samari da ‘yammata ana kalankuwa, ana darawa, ana tafawa ana murna, da farin ciki. Yara kuma su yi ta zaci sunakai da komowa harwajen kwanabiyar ko bakwai.
Yawon Sallah: Mutane suna zuwa suna gai da ‘yan’uwa da abokai da surukai, don taya su murnar kewayowar ranar sallah. Su kuma sukan ba su goron sallah. Yara da yawa sukan mayar da yawonsalla tamkar wani abin ku zo ku gani suna shiga gida-gida, suna kaɓiar abin yawon sallah, kuma suna tafiya suna yi wa juna ba’ar raha iri -iri.
Rana ta biyu, a kashegarin sallah, sai sarki yakan yi hawa, wanda ake kira hawan sarki, ya kuma ci gaba da hawan har kwana uku don ya sadu da mutanensa, ya ga wasu wurare. Wannnan hawa, a wasu wurare sunansa hawan daushe , ko hawan bariki.
Shi ke nan, sai a ci gaba da shagulgulan sallah har ‘yan kwanaki, sa’annan kowa ya koma ga harkar gabansa ta yau da kullum.
“Sallah bukin ɗaya rana! Sallah mai yawan baya, kin wuce kin bar wawa da bashi!”

AL'ADU

AL’ADUN HAUSAWA

Hausawa mutane ne masu tsananin rikon al’adunsu na gargaiiva, musamman wajen tufafi, da abinci, da al’amuran da suka shafi aure ko haifuwa, ko mutuwa, da sha’anin mu’amala tsakanin dangi da abokai da sbuwagabaam da sauransu, da kuma al’amuran sana’a ko kasuwanci ko neman ilimi.
Tun daga zuwan Turawa har yau, Hausawa suna cikin al’ummomin da ba su saki tufafinsu na gargajiya su ari na baki ba. Galibin adon namiji a Hausa ba ya wuce riga gari, da wando musamman tsala, da takalmi faɗe ko ƙafa-ciki, da hula ƙube, ko dankwara, ko dara. In kuma saraki ne ko malami ko dattijo, yakan sa rawani. Adon mata kuwa, zane ne, da gyauton yafawa, watau gyale, da kallabi, da taguwa, da ‘yan kunne, da dutsen wuya, watau tsakiya. A da can, suna sa ɗan hanci, amma yanzu wannan adon ya ƙaura.
Yawancin abincin Bahaushe kuwa, ana yin sa da gero ko dawa ne. Sai kuma sauran abubuwan haɗawa, da na marmari, kamar su wake da shinkafa da alkama, da kayan rafi, da sauransu.
Yawancin Hausawa Musulmi ne, saboda haka yawancin al’adunsu da suka shafi aure da haifuwa da mutuwa, duka sun ta’allaƙa da wannan addini. Sai ɗan abin da ba a rasawa na daga al’adun gargajiya, musamman a wajen Maguzawa.
Haka kuma wajen mu’amala da iyaye ko dangi ko abokai, ko shuwagabanni ko maƙwabta ko wanin waɗannan yawanci na Musulunci ne. Kazalika sha’anunuwan sana’a da kasuwanci da neman ilimi, duk ajikin Musulunci suka rataya,
Can ainihi, sana’a da kasuwanci da neman ilmi suna bin gado ne. Watau kowa yana bin wadda ya gada kaka da kakanni. Kuma idan mai sana’a ya shiga baƙon gari, zai je ya sauka a gidan abokan sana’arsa ne. In ma koyo ya zo yi, zai je gidan masu sana’ar gidansu ne. Saboda haka kusan kowace sana’a akwai sarkinta, da makaɗanta, da mawaƙanta, kai har ma da wasu al’adu na masu yinta da suka sha bamban da na sauran jama’a.
Bauta da barance a wurin Bahaushe ba munanan abubuwa bane, musamman dangane da sha’anin koyon sana’a. Bawa yana fansar kansa ta hanyar sana’a. Kuma mai koyon sana’a yana yin barance a gidan mai koya masa ne. Irin wannan almajircin, ana kiran sa bauta. Duk mai wata sana’a, ko ɗan kasuwa, ko malami, yana alfaharin a ce ga wasu sun koya a wurinsa har sun ƙasaita, ko ma har sun fi shi. Su kuma duk irin maƙamin da suka samu, ba za su raina shi ba. Za su riƙa yi masa ladabi.

SALLOLI BIYAR NA YINI SUNA KARA LAFIYA MAI INGANCI GA JIKIN DAN ADAM.

SALLOLI BIYAR NA YINI SUNA KARA LAFIYA MAI INGANCI GA JIKIN DAN ADAM.  Hakika Salloli biyar da mukeyi ayini a kowace suna  karawa dan Ada...